Kano: ‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Basarake a Jihar

Masarautar Karaye da ke jihar Kano ta sanar da satan matar sarkin kauyen Tsara da ke karamar hukumar Rogo

A ranar Juma’a da misalin karfe 1 na dare ‘yan bindiga suka fada gidan sarkin kauyen da bindigogi suka tafi da matarsa – Har yanzu ba’a fahimci dalilinsu na yin hakan ba, don basu kira kowa sun sanar da kudin da suke bukata ba Masarautar Karaye da ke jihar Kano ta sanar da satan matar sarkin kauyen Tsara da ke karamar hukumar Rogo, Aishatu Aliyu da wasu ‘yan bindiga suka yi. Kamar yadda sarkin Rogo (Wamban Karaye), Muhammadu Mahraz, ya kai wa Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II, rahoto, wasu ‘yan bindiga sun shiga gidan sarkin kauyen Tsara, Aliyu Muhammad, da misalin karfe 1 na daren Juma’a, inda suka tafi da matarsa
Kakakin masarautar, Haruna Gunduwawa, ya sanar da PREMIUM TIMES cewa ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka yi ta harbin iska kafin su dauki matar a gaban sarkin kauyen. A cewarsa, sai da mazauna kauyen suka ga alburusai 17 washegarin faruwar lamarin. Ya bayyana yadda da yawan ‘yan kauyen suka kwana a daji a daren da lamarin ya faru don gudun mutuwa.
Gunduwawa yace, har safiyar Talata, Masarautar ba ta fahimci dalilin satar matar ba, don har yanzu ba su kira kowa ba balle su sanar da kudin da za’a fanshe ta. Kakakin Masarautar ya ce yanzu haka kusan mutane 4 kenan da aka yi garkuwa da su cikin watanni 2 a karamar hukumar Rogo, wacce iyaka ce tsakanin jihar Kano da Kaduna. Yace sarkin karaye ya roki jami’an tsaro da su duba al’amarin kuma su dauki mataki a kai. Ya kuma roki jama’a da su taya masarautar da addu’a don samun tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here