Bata Gari Sun Fasa Shagon Mansura Isah a Kano

Bata gari sun fasa shagunan mutane a garin Kano ciki har da shagon tsohuwar arumar Kannywood, Mansura Isah
Matasan wadanda suka fake da zanga-zangar EndSARS sun kwashe komai da ke ciki shagon jarumar – Mansura ta bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan sun hade kayayyakin dukka shagunansu a waje daya Wasu matasa da ake zaton bata gari ne a birnin Kano, sun kai mamaya shagon tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isa da ke jihar. Bata garin sun fasa shagon nata da ke kan titin Filin Jirgin Sama daura da titin Ahmadiyya, inda suka yashe komai da ya ke ciki. Mansura wacce ta kasance mata ga fitaccen jarumin masana’antar, Sani Musa Danja, ce ta wallafa bidiyo da hotunan shagon da aka fasa mata a shafinta na Instagram
Ta wallafa a shafin nata cewa “Mun tattara kayanmu da ke ragowar sauran ofishinmu da ke unguwar Badawa zuwa wuri daya domin rage wa kanmu wahala akoda yaushe ta hanyar zirga-zirga daga wannan shagon zuwa wancan. Ofishinmu na @todays_life_foundation da ke Badawa layout, da shagonmu na daukar hoto @celebrityphotos2442 da kuma tsohon shagona da ke Audu Bako. “Mun kwashe komai da ya ke shagon kama daga Takalma, jakunkuna, Firji, AC, Talabin da sauran kayayyaki daga tsoffin shagunan zuwa wannan sabon shagon domin mamallakan shagunan sun bukaci mu bar masu wajensu tunda ba za mu sake biyan haya ban a wata shekarar. Amma sunsace komai, basu bar ko takalmi daya ba. Sun kwashe komai da komai. Amma mun fawwala wa Allah komai
“Dama mun san mutane suna neman dama irin wannan ne domin su aikata mummunan laifuka, sun fake da zanga-zangar #EndSARS da kuma #EndInsecurity don su lalata dukiyoyin jama’a da rayukan mutane.” “Amma ina addu’a ga samun sabuwar Najeriya kuma muna yi wa kasarmu addu’an samun zaman lafiya. Alhamdulillah da kasancewa da lafiya da rayuwa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here