Home DUNIYA Legas: Yadda Wasu jama’a su ka Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Tallafin Korona

Legas: Yadda Wasu jama’a su ka Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Tallafin Korona

0

Legas: Yadda Wasu jama’a su ka Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Tallafin Korona

 

    Tirmitsitsi ya barke a Lagos, yayin da cincirindon mutane su ka fasa wani sito da aka ajiye kayan tallafin korona su ka rika jidar kayan abinci, a Monkey Village da ke Maza-maza, cikin unguwar Odofin.

Kayayyakin da aka rika jida din dai duk an buga masu tambarin ‘COCAVID’, NOT FOR SALE; wato kayan tallafin korona ne, ba na sayarwa ba ne.

Kayayyakin sun hada da shinkafa, macaroni, taliya, gishir, garri, sukari da kuma katan-katan na indomi.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa tun safe mazauna unguwar ke ta jidar kayan abincin.

“Da farko dai wasu mutane ne su ka isa sito din da safe su ka dauki wasu kayayyakin abincin. Dama sun saba zuwa kowane lokaci su na kwasa.” Haka wani mazaunin unguwar wanda ya roki kada a bayyana sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES.

“Lokacin da mutanen su ka lodi kayan abinci za su tafi, sai aka rika rokon su su bai wa wadanda ke wurin, amma su ka ki. Bayan sun tafi sai aka taru aka fasa sito din, kowa ya rika jida kawai. Gwamnati ta kimshe abinci, ba ta raba ba, ga kuma jama’a na cikin halin kunci.”

 

 

 

 

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest News
Firaiministan Isra'ila ya yi Barazanar ƙwace Yankunan GazaMutane 14 sun Mutu, 886 Sun Kamu da Cutar Kwalara a Najeriya - NCDCSojojin Sudan sun ƙwato Filin Jirgin Saman Khartoum Daga Hannun Dakarun RSFAllah ya yi wa Abdullahi Tanka Galadanci RasuwaBabu Tabbas ko Zan Tsaya Takara a Zaɓen 2027 - Atikuƙungiyar Boko Haram ta Kashe Sojoji da Dama a BornoNatasha: An yi sa-in-sa a Majalisar DattawaHajji/Umara: Ana Ci gaba da Jan Hankalin Masu ɗauke-ɗauken Hoto a HaramiAn Rantsar Janar Tchiani a Matsayin Shugaban Riƙo na Jamhuriyar NijarƘudurin Cire Kariya ga Gwamnoni ya Tsallake Karatu na Biyu a Majalisar WakilaiAƙalla Falasɗinawa 85 ne Suka Rasa Rayukansu a Sabon Hare-Haren Isra'ilaƳan Bindiga sun yi Awon Gaba da Gomman Fasinjoji a HabashaHamas ta Harba wa Isra'ila Rokoki UkuNimet ta yi Gargaɗi Kan ɓullar Cutar SanƙarauShugaba Tinubu ya Yaba wa Majalisa Kan Tabbatar da Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas