ENDSARS: Gidajen Rediyo dana Talabijin na NBC na gargaɗi kan yaɗa bidiyon zanga-zangar
Read Also:
Hukumar da ke lura da ayyukan gidajen rediyo da talabijin ta Najeriya NBC, ta gargaɗi kafafen watsa labarai da su yi taka-tsan-tsan wajen nuna hotunan bidiyon da jama’a suka yada a shafukan sada zumunta kan ci gaba da zanga-zangar EndSARS.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Tuwita, NBC ta ce ya kamata kafafen yada labarai su riƙa lura da abin da suke yaɗawa don kaucewa muzanta mutane da hukumomin gwamnati da kuma ƙungiyoyi