ENDSARS: Gbajabiamila Yace Ko Shakka babu Sojoji Sun Hallaka Masu Zanga-Zangar

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila, ya ce babu shakka dakarun sojin kasar sun hallaka masu zanga-zangar End SARS a jihar Legas.

”A bayyana take cewa an kashe mutane, kuma an raunata wasu da dama” in ji shi.

Lamarin dai ya faru ne ranar Talata, lokacin da masu zanga-zangar suka taru a Lekki, in da jami’an soji suka ritsa su.

Da farko dai gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu ya musanta cewa an kashe ko da mutum guda a yayin aukuwar lamarin, kafin daga bisani ya wallafa wani sako a shafinsa na tuwita, in da yace mutum guda ya mutu a gadon asibiti.

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin jami’an tsaro da ke musanta cewa sun hallaka jama’a, da gwamnati da fitar da sanarwa biyu, da kuma masu ganin cewa an kashe mutane kawai dai ana kokarin boyewa ne

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here