Ki Daina Yaudarar ‘Yan Najeriya da Mabiyanki ta Hanyar Amfani da ni Kina Hada Karairayi – Tsohon Mijin Jaruma Mai Kayan Mata

Tsohon mijin fitacciyar mai siyar da kayan mata, Jaruma, Fahad ya bayyana cewa yana kula ta ne kawai saboda dan shi da ke hannunta.

Matashin ya bayyana cewa ya bar Jaruma duk da burga da dukan kirjin da take yi kan kayan matanta wadanda yace basu aikin komai.

Fahad ya shawarci Jaruma da cewa ta daina yaudarar ‘yan Najeriya da mabiyanta ta hanyar amfani da shi tana hada karairayi.

Fitacciyar mai siyar da maganin mata, Jaruma, wacce ta kasance a kanun labarai kowanne mako,ta sha bajiya daga tsohon mijinta a kafar sada zumunta ta Instagram.

A wata wallafa da aka gani a Instagram, Fahad ya yi bayani kan cewa aurensa da Jaruma ya kare kuma shi ya fara barinta tare da yin watsi da lamarinta.

Ya cigaba da cewa, yana tuntubar mai siyar da kayan matan ne saboda dan shi da ke hannunta kuma ya dace ta daina yaudarar mabiyanta.

Fahad ya kara da wallafa hoton sakon da ya tura wa tsohuwar matarsa domin samun su yi magana, amma yace ta wallafa domin neman nuna cewa yana bibiyarta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here