Dakarun Sojin Kasa Sun Hallaka Gawurtaccen ‘Dan Kungiyar ‘Yan Awaren IPOB/ESN a Jahar Imo

Dakarun birged ta 34 na Manyan Bindigogi ranar Lahadi 17 ga watan Afrilu 2022 sun samu nasarar hallakar da gawurtaccen d’an haramtacciyar k’ungiyar y’an awaren IPOB/ESN a yankin Ihioma na k’aramar hukumar Orlu a jihar Imo.

Dakarun da ke sintiri sun samu tsagerun ne suna harbi cikin iska a mahadar Banana domin tsorata Jama’a da kuma tilasta masu zaman gida. Tsagerun bayan hango dakarun mu, sai suka tsere a mota k’irar Toyota Highlander domin sake shiri.

Bayan fafatawa mai tsawo dakarun mu sun samu nasarar hallakar da jagoran tsagerun, inda sauran suka tsere. Dakarun mu tuni suka mamaye yankin domin ganowa da magance sauran tsagerun.

Bayan shan kashi a hannun dakarun mu, tuni tsagerun suka fara neman amincewar al’umma ta han’yar yad’a wani bidiyon farfaganda. Muna kuma kira ga al’umma da su yi watsi da farfagandar baki d’ayan ta.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu
Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasan Najeriya
18 Afrilu 2022

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here