NHGSFP: FMHADMSD ta Samu Yardan Ɗalibai a Makarantun Gwamnati 

 

Shirin National Home Grown School Feeding Programme na kasa, wani babban shiri ne kuma daya ne daga cikin shirye-shirye masu kayatarwa na Ma’aikatar jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma na tarayya, kuma ba shakka daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta cimma.

Shirin ya kunshi jihohi 35 na Najeriya da kuma Abuja, tare da jihar Bayelsa da zai zo nan ba da jimawa ba, kuma kusan dalibai miliyan 9.8 dake makarantun firamare na gwamnati 53,000 a fadin kasar, ke cin gajiyar shirin.

Tun daga shekarar 2019 bayan samar da ma’aikatar, shirin ya zarce duk wani shirin ciyar da Makarantu a fadin Afirka baki daya, ta hanyar zama mafi girma a nahiyar.

Shirin ya samowa kasar yabo na musamman, kuma ba shakka a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ne aka samu shirin ciyar da dalibai na farko a kasar tun 1999. Wa zai yi tunanin akwai ranar da gwamnatin tarayya za ta ciyar da daliban makarantun gwamnati a Najeriya ?. Kar na manta cewa abincin da ake bawa daliban, abinci ne mai gina jiki kuma an tsara shi ne don yaki da rashin abinci mai gina jiki.

Na hadu da iyayen yara da yawa, a wani lokaci a cikin shekarar 2010, na yi musu gargaɗi game da illar rashin sa yaransu a makaranta. Amma Duk da haka, shawarar ta gaza, musamman ilimin da ya shafi yara mata. Uzurin su akoyaushe shine rashin samun damar sa yaran nasu a makarantu.

Sun gwammace su aurar da yaran nasu matan tun suna kanana, sannan su tura samarin kan titi su yi tallan ruwan sha.

Baya ga haka a shekarar 2019, an sanya ni sake komawa wajan da naje a shekarar 2010, akan naje na bada shawara, ga mamakina, yawan ɗaliban dake shiga makaranta sun karu da kashi 90%, nayi mamaki matuƙa, sai na hadu da wata tsohowa, dake da jikoki biyar dukkan su sun haura shekaru 10, Na tambaye ta lafiyar su, sai ta rike hannuna ta ce da ni “kai ɗana, a kodayaushe mun kasance masu son samarwa yaramu ilimi, amma ba mu taba samun hanyar shigar da ‘ya’yan mu makaranta ba, Allah ya karbi addu’o’in mu. Yanzu gwamnati tana ciyar da ’ya’yan mu, kuma an raga mana dawainiyar kashe kuɗi.

A nan ne sai na gane cewa, matsalar ba ta ilmantar da su ba ne, domin Nijeriya ta dade, tana kan tsarin ilimin kyauta, sai aka yi amfani da dabarar da aka jawo hankalinsu, don su amfana da ilimin kyauta.

Shirin National Home Grown School Feeding programme, na Ƙasa ba kawai ya ƙara yawan adadin yara ɗalibai masu son shiga makarantu bane, sai dai Ya kawo saukin karatu da jin dadi, yaki da yunwa da rashin abinci mai gina jiki, da kuma magance matsalar rashin aikin yi ta hanyar samar wa sama da mutane 107,000 aikin dafa abinci da ayyukan yi.

A duk Lokacin da ake magance rashin aikin yi, ana kuma magance yawan talauci ne. A iya jihar Kano, yawan daliban da suka shiga makaranta ya karu daga miliyan 1.2 zuwa miliyan 2.1 bayan bullo da shirin da ma’aikatar jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma ta tarayya, a cikin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here