Fadar Shugaban Najeriya ta yi Karin Bayyani Kan Jirgin Yakin Super Tucano

Fadar shugaban Najeriya ta kare matakin ta na jan kafar tura jirgin yaki samfurin Super Tucano, domin yakar barayin daji masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa arewa maso gabashin kasar.

Fadar ta ce, kafin gwamnati ta sayi jiragen yakin daga Amurka, akwai yarjejeniyar da za a cimma gabannin cinikin, yadda Najeriya ba za fada bakin littafin kasar ba kan batun take hakkin dan adam.

Mai magana da yawun shugaban kan harkar yada labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a tashar talbijin ta Trust.

Jaridar Vanguard ta ambato Garba Shehu na cewa: ”Ana bai wa sojoji horon soji ne, shugaban kasa ya san abin da ya ke yi. Fatan mu da zarar ya kammala aikin nan ya koma gida, ba kotun manyan laifuka ta duniya ta gayyace shi saboda take hakkin dan adam ba. Don haka mu bar sojoji su yi komai bisa tsari, kuma tsari irin na su a lokacin da ya dace.

Idan ka na mu’amala da kasashe kamar Amurka, ya zama dole ka bibiyi ra’ayin jama’a da kare hakkinsu wannan ya na da matukar muhimmanci agare su. A bayyane ta ke karara, sun saidawa Najeriya jiragen yaki samfurin Super Tucano, amma ana bin tsarin da dokoki suka tanada wajen tabbatar da hakan.

Ka da ku manta tsohuwar gwamnatin Amurka ta Brack Obama ta ki saidawa Najeriya jiragen yaki saboda zargin take hakkin dan adam, amma shugaba Buhari ya yi kokarin ganin an wanke wannan zargin. Don haka wannan ma za a yi amfani da su a lokacin da ya dace,” in ji Garba Shehu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here