Ayatollah Khamenei: Sakamakon zaɓen Amurka “ba zai sauya manufofin Iran ba

Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya jaddada cewa sakamakon zaɓen Amurka ‘ba zai sauya’ manufofin Iran ba kan Amurka.

“Manufarmu… a bayyane take. Sauyin wani ba zai sauya komi ba,” in ji shi. “Ba ruwanmu da wanda zai zo ko zai tafi.”

Donald Trump ya yi “matsin lamba” ga Iran a yaƙin neman zaɓensa tun yin watsi da yarjejeniyar nukiliya a 2018.

Abokin hamayyarsa, Joe Biden, ya ce zai iya dawo da yarjejeniyar.

Yarjejeniyar wacce aka ƙulla a 2015 lokacin da Mista Biden yake matsayin mataimakin Shugaba Barack Obama, ta sa an sassauta wa Iran takunkumai domin dakatar da shirinta na nukiliya, wanda ta ce na bunƙasa makamashi ne.

Shugaba Trump ya ce “tana da naƙasu” tare da dawo da takunkumin da ya gurgunta tattalin arzikin Iran a kokarin tilasta mata sake yarjejeniyar.

Iran ta ƙi yadda da hakan tare da mayar da martani ta hanyar dawo da wasu ayyukanta na nukiliya.

Ƙasashen biyu sun kusan abkawa yaƙi a watan Janairu bayan da Mista Trump ya bayar da umurnin kai hari ta sama a Iraki wanda ya kashe babban kwamandan Iran Qasem Soleimani wanda ya zarga da jagorantar kashe dakarun Amurka.

Iran ta mayar da martani inda ta harba babban makami mai linzami a sansanin dakarun Amurka a Iraki. Sai dai babu wani Ba’amurke da harin ya kashe, amma sama da 100 ne suka samu matsalar da ta shafi ƙwaƙwalwa.

Ayatollah Khamenei ya gabatar da jawabi ne yayin cika shekara 41 da ƙwace ofishin jekadancin Amurka a Tehran da wasu ɗliban Iran suka yi, inda suka yi garkuwa da Amurkawa 444.

Tun lokacin hulɗar diflomasiya ta katse tsakanin Iran da Amurka.

“Ana zaɓe a Amurka. Abubuwa za su faru, amma ba su dame mu ba,” a cewar jagoran na Iran, wanda shi ke jan akalar rundunar sojin ƙasar da kuma dukkanin harakokin da suka shafi ƙasar.

Ayatollah Khamenei ya yi wa Amurka shaguɓe inda ya ce shugaba mai ci ya yi gargadin cewa zaɓen ƙasar shi ne “wanda aka fi yin maguɗi a tarihi.

“Wannan ce dimokuraɗiyyar Amurka,” in ji shi.

A wata hirarsa ta CBS a ranar Litinin, ministan harakokin wajen Iran Javad Zarif ya ce Iran ba ta da wani ɗan takara da take so.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here