Na Zabi Ci gaba  – Matar Gwamna Zulum

Uwargidan gwamnan jihar borno, habiba babagana umara zulum ta zabi mijinta a karo na Biyu a maiduguri a mazabar shariff tijjani lungun kanurai a Bolori.

In da ta bayyana ra’ayinta na yin APC SAK, a zaben gwamna da ‘yan majalisun jiha.

Habiba ta bayyana zaben  a matsayin  ci gaban jihar Borno.”

“Mijina yana aiki tuƙuru kuma kowa ya san yana ƙaunar mutanensa sosai. Don haka ina jira kawai a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.”

Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar Borno cewa Gwamna Zulum zai rubanya kokarinsa na gyara Borno da kuma karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here