Abinda Toshe Iyakokin Kasa ya yi wa Mana – Shehu Sani

 

Shehu Sani ya soki rufe iyakoki da aka yi na tsawon wata-da-watanni.

Tsohon ‘Dan majalisar yana ganin ba muci ribar komai da matakin ba.

Sani yace noman shinkafa ya damu gwamnatin tarayya ba wani abu ba.

Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi magana game da rufe iyakokin Najeriya da aka yi, ya ce hakan bai taimaka wa kasar da komai ba.

Shehu Sani ya rubuta a Twitter cewa: “Rufe iyakokinmu da mu kayi bai yi wani tasiri wajen dakile hare-haren ‘yan bindiga da kuma ta’addanci ba.”

Sani ya ce: “Bal ma, sai dai ya ta’azzara wahala da masifa a kan mutanen da ke kan iyakoki.”

A cewar tsohon ‘dan majalisar, yunkurin hana shigo da shinkafa ya sa gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasa ba komai ba, kuma ba a ci riba ba.

“Illa-iyaka, maganar shinkafa ce kawai, bai wuce nan, kuma har yanzu bamu cikin wadanda suka fi kowa noma ko fitar da shinkafa waje.” Inji Sani.

Shi kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da gwamnoni cewa ya garkame iyakokin kasar ne domin dakile shigowar makami da kwayoyi.

Ya ce: A zama na da gwamnonin jihohi yau (jiya), na yi bayanin cewa an rufe iyakokin kasa ne domin ayi maganin fasa kaurin makamai da kwayoyi.”

Mai girma Muhammadu Buhari yake cewa tun da makwabtan Najeriya sun fahimci wannan yunkuri, gwamnati za ta bude iyakokin kwanan nan.

Ra’ayin Sani ya sha ban-bam da na shugaban Najeriyar, ya ce yunkurin bunkasa noman shinkafa ya jawo aka rufe iyakokin Najeriya ba maganin tsaro ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here