Mulkin Soja: ALLAH ya yi wa Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya, Ahmed Joda Rasuwa

 

Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya lokacin mulkin Soja kuma mutum na farko da Buhari ya ba mukami bayan nasara a 2015 , Alhaji Ahmed Joda, ya mutu.

BBC ta ruwaito daya daga cikin ‘yayan marigayin, Asma’u Joda, ta bayyana cewa mahaifinta ya rsu ne yau Juma’a a Yola, babbar birnin jahar Adamawa.

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Alhaji Ahmed Joda ya cika ne yana mai shekaru 91 a duniya.

A cewar DT, Ahmad Joda ya rasu ne bayan jinya a asibitin FMC Yola.

Joda ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Birtaniya inda ya halarci Kwalejin Pitmans da ke birnin London daga 1954 zuwa 1956.

Ya rike kujeran sakataren din-din-din lokacin gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon (Mai murabus).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here