Dalilin da Yasa na Ajiye Aikina a Matsayin Mai Magana da Yawun Tinubu – Ngelale

 

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya sanar da ajiye aikinsa ‘na wucin gadi’

Cikin wata sanarwa da mista Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a ranar Juma’a ya miƙa takarda zuwa ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila domin sanar da shi aniyarsa ta tafiya hutun da bai san lokacin ƙarewarsa ba, don mayar da hankali kan rashin lafiyar wasu iyalansa da bai bayyana ba.

”Na yi hakan ne domin samun isasshen hutun da zai ba ni damar mayar da hankalina kan matsalolin rashin lafiya da a yanzu haka iyalaina ke fuskanta”, in ji Ngelale.

Mista Ngelale ya kuma ce ya jingine duka sauran muƙaman da yake riƙe, da suka haɗar da wakilin Shugaban ƙasa na musammman kan sauyin yanayi da kuma shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan inganta muhalli.

”Na ɗauki wannan mataki ne bayan shafe kwanaki ina tuntuɓar iyalai da dangi kan yanayin rashin lafiya da ake fuskanta a gidanmu”, in ji shi.

Daga ƙarshe ya ce yana sa ran dawowa domin ci gaba da aikinsa, idan lokaci da rabo sun ba shi damar hakan.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here