Mafi ƙarancin Albashi: Gwamnan Akwa Ibom ya Amince da N80,000

 

Gwamnan jihar Akwa Ibom Umo Eno ya sanar da fara biyan ma’aikatan jihar naira 80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi,

Gwamnatin jihar ta kuma kafa kwamitin tabbatar da tsarawa tare da tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin, inda gwamnan ya ba su wata ɗaya su kammala aikinsu.

Ini Ememobong, kwamishinan watsa labarai na jihar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce wannan matakin na cikin burin gwamnan ta inganta rayuwar ma’aikatan jihar da jin daɗinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here