Ahmed Aliyu ya Lashe Tikitin Takarar Gwamna a Jihar Sokoto
Sakamakon zaben fidda gwani daga jihar Sokoto ya fito, an bayyana sunan Ahmed Aliyu a matsayin wanda ya lashe zabe.
Wannan na zuwa ne bayan ‘yar hatsaniya da aka samu a harabar zaben daga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da sanar da sunayen wadanda suka lashe zaben fidda gwani na APC a jihohin kasar nan.
Jihar Sokoto – Tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Sokoto, TVC ta rawaito.
Aliyu, ya samu kuri’u 1,080 daga cikin jimillar kuri’u 1,182 da aka kada a zaben fidda gwani da ‘yan takara shida suka fafata a ciki.
Read Also:
Shugaban kwamitin zaben, Aliyu Kyari, ya ce Ibrahim Gobir ya samu kuri’u 36, Faruk Malami-Yabo ya samu kuri’u 27, sai kuma tsohon ministan sufuri, Yusuf Suleiman ya samu kuri’u 16 da kuri’u 23 da kuma kuri’un da suka lalace.
Kyari ya ce sauran ‘yan takarar sun hada da Abubakar Abdullahi mai kuri’a 1 da Sen. Umar Gada mai kuri’u zifiri.
Shugaban ya bayyana Aliyu ne da mafi yawan kuri’u a matsayin wanda ya yi nasara bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
Deliget-deliget da sauran masu ruwa da tsaki sun koka kan tsarin da kuma yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin, inji rahoton Vanguard.
Sauran ‘yan takaran dai sun nuna damuwa kan bata kusan sa’a guda a yayin gudanar da zaben.
Ambasada Malami-Yabo, Suleiman da Abubakar sun mika kokensu ga ‘yan kwamitin, inda suka bukaci dukkanin manyan jiga-jigan da ake zargin suna tsoratar da deliget da su fice daga harabar domin tabbatar da an samu daidaito.
An kuma dakatar da ayyukan na tsawon sa’o’i kan muhawarar da ta bullo yayin da ‘yan takarar suka yi kira ga kwamitin da ya bi hanyoyin da suka dace.