Amurka da Jamus na Son Jurgen Klopp, AC Milan na Zawarcin Pavlovic

 

Amurka da Jamus na son tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp, dan wasan baya na Bayern Munich Matthijs de Ligt na son komawa Manchester United, Crystal Palace ta kuduri aniyar ci gaba da rike Eberechi Eze.

Kasar Amurka na son tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp ya maye gurbin Gregg Berhalter a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar. (Independent)

Sai dai Klopp din ba ya sha’awar Amurka, kuma yana son hutu ne a yanzu. (Athletic)

A gefe guda ita ma kasarsa wato Jamus ma na neman mai horarwar (Team Talk)

Al-Ittihad na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Aston Villa dan kasar Faransa Moussa Diaby, mai shekara 25. (Yahoo)

Al-Ittihad na tattaunawa da dan wasan Manchester United dan kasar Brazil Casemiro, mai shekara 32. (L’Equipe)

Dan wasan baya na Bayern Munich dan kasar Netherlands Matthijs de Ligt, mai shekara 24, yana son komawa Manchester United nan take. (Sky Sports)

Bayern na son Yuro miliyan 50 (£38.7m) kan De Ligt. (90mint)

Crystal Palace ta kuduri aniyar cewa ba za ta siyar da dan wasan Ingila Eberechi Eze mai shekaru 26 ga Tottenham ko Manchester United ba. (Football Insider}

Nice na sha’awar dan wasan baya na Luton Town mai shekaru 22 Teden Mengi. (Foot Mercato)

Arsenal ta kai kudin na gani ina so, na golan Ajax dan kasar Ingila Tommy Setford mai shekaru 18. (Fabrizio Romano)

Benfica ta ki amincewa da tayin da Paris St-Germain da Manchester United suka yi wa dan wasan tsakiyar Portugal Joao Neves mai shekaru 19. (A Bola}

AC Milan na zawarcin dan wasan bayan RB Salzburg dan kasar Serbia Strahinja Pavlovic, mai shekara 23, wanda Newcastle ke nema. (Calciomercato)

West Ham ta kawo karshen fatan Manchester City na dauakr dan wasan tsakiyar Ingila Chinaza Nwosu mai shekaru 16, inda za ta ajiye shi a karamar kungiyar. (Football Insider)

Chelsea ta kawo karshen zawarcin dan wasan gaban Atletico Madrid dan kasar Sipaniya Samu Omorodion mai shekaru 20. (Marca Spanish)

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here