Kano: APC na Koƙarin Hana Abba Mulki – NNPP

 

Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta zargi APC da yunƙurin kwace mulki ta kowane hali a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.

A wata sanarwa da kakakin NNPP na ƙasa ya fitar, jam’iyyar ta tona yadda APC ke amfani da shari’a da jami’an tsaro don tayar da zaune tsaye a jihar.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan APC ta buƙaci jami’n tsaro su kama jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Jihar Kano – New Nigeria People’s Party (NNPP) da jam’iyyar APC sun fara musayar yawu da zargin juna game da rikicin da ke faruwa a jihar Kano.

Awanni bayan APC ta buƙaci a kama Rabiu Kwankwaso saboda kalaman da ya yi, NNPP ta fito ta caccaki jam’iyyar da cewa ta cika ƙwaɗayin mulki.

NNPP mai kayan marmari ta zargi APC da yunƙurin kwace mulki da ƙarfi daga hannun zaɓin al’umma, Gwamna Abba Kabir Yusuf, Vanguard ta ruwaito.

Jam’iyya mai mulkin Kano ta yi wannan zargi ne a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar yau Laraba.

A cewarta, matakin sauya dokar masarautar Kano da mayar da Muhammadu Sanusi II kan mulki ya ƙara fito da yadda APC ke tsananin son mulki.

APC na koƙarin hana Abba mulki

Jam’iyyar NNPP ta kuma yi zargin cewa APC na amfani da bangaren shari’a da jami’an tsaro wajen gurgunta tsarin dimokuradiyya da tada zaune tsaye a jihar.

Ta yi kira ga ƴan Najeriya su farka daga barci kana su toshe duk wata hanya da APC ke kokarin bi domin wargaza zaman lafiyar Kano da ƙwace mulki ba bisa ka’ida ba.

A sanarwar, NNPP ta ce:

“APC ba ta ɓoye mugun nufinta na hana wanda ya lashe zaɓen 18 ga watan Maris, 2023, Abba Kabir Yusuf gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali ba.”

“Yaushe aka tuge gwamna daga matsayin shugaban tsaron jiharsa? Mutanen Kano ba za su bari wanda suka zaɓa ya wulaƙanta ba, za su kare shi duba da abubuwan alherin da yake zuba masu.”

Channels tv ta kawo rahoto cewa APC ta buƙaci jami’an tsaro su cafke jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso bisa zargi barazana ga tsaron Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here