Arsenal ta Sayi Calafiori Daga Bologna

 

Arsenal ta sayi ɗan wasan bayan tawagar Italiya, Riccardo Calafiori daga Bologna kan fan miliyan 42 ciki har da tsarabe-tsarabe.

Ɗan wasan mai shekaru 22, wanda ya buga wasa uku a cikin rukuni a gasar nahiyar Turai a Euro 2024, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da Gunners.

Nan take yana tare da ƴan wasan Arsenal da ke buga wasannin sada zumunta, domin tunkarar kakar bana da take yi a Philadelphia.

Calafiori na iya taka leda a matsayin mai tsaron baya daga tsakiya ko kuma daga gefen dama – wanda a baya ya buga gaba daga gefen dama.

Ya buga wa Bologna wasa 30 a gasar Seria A ta bara, inda ya ci kwallo biyu ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.

Bologna ta kare a mataki na biyar a teburin Serie A kakar da ta wuce da samun gurbin Champions League da za a buga a bana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here