Atiku ya Magantu Kan Hukuncin Kotun ƙoli da ta Yanke na ƙananan Hukumomi

 

Alhaji Atiku Abubakar ya nuna farin ciki bisa hukuncin da kotun ƙolin najeriya ta yanke na ƴantar da ƙananan hukumomi daga hannun gwamnoni 36.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ayyana hukuncin a matsayin wata babbar nasara ga ƴan Najeriya.

Sai dai duk da haka Atiku ya nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ke katsa landan a harkokin tattara kudin shigar kananan hukumomi.

Alhaji Atiku ya faɗi haka ne yayin da yake martani bayan hukuncin kotun ƙoli a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Twitter.

Atiku ya mayar da martani

Da yake nuna goyon bayansa kan hukuncin, Atiku ya ce:

“Ina tare da hukuncin da Kotun Koli ta yanke na cewa tsarin mulkin Najeriya ya kasu zuwa mataki uku, kuma daga cikinsu kananan hukumomi ya kamata su zama cibiyoyin ci gaba.”

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira da a bai wa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu ta kowane ɓangare fiye da rabon kuɗin shiga daga tarayya.

“Ina ganin ba a iya kason kuɗi daga tarayya kaɗai ya kamata mu ƴantar da ƙananan hukumomi ba, har da batun tattara kuɗaɗen shiga, shi ma a ba su ƴanci,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here