An Bankado Yawan Asusun Bankin da Samuel Ortom ya ɓoye Kafin ya Bar Mulki
Gwamnatin jihar Benuwai ta bankaɗo badaƙalar yawan asusun bankin da Samuel Ortom ya ɓoye kafin ya bar mulki.
Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafi, Michael Oglegba, ya ce sun gano jihar tana da asusu sama da 600 amma 25 aka nuna wa sabon gwamna.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Alia na APC ta gaji bashin kuɗi N359bn wanda ya kunshi basukan kananan hukumomi.
Jihar Benue – Gwamnatin jihar Benue ta zargi tsohuwar gwamnatin da ta shude ta tsohon gwamna Samuel Ortom na PDP da yin amfani da asusu sama da 600.
Gwamnatin Benuwai karkashin Gwamna Hyacinth Alia na APC ta caccaki Ortom da ɓoye bayanan asusun banki sama da 570, inda ya nuna 25 kacal sa’ilin miƙa mulki.
Read Also:
Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafin kuɗi na jihar, Michael Oglegba, ne ya faɗi haka yayin da tawagar ƙungiyar ‘yan jarida (NUJ) ta kai masa ziyara a Ofis ranar Talata a Makurɗi.
Ya ce bisa wannan dalili ne mai girma Gwamna Alia ya bada umarnin rufe dukkan asusun gwamnati bayan ya karɓi mulki, Daily Trust ta ruwaito.
Yadda gwamnatin Alia ta tono ragowar asusun Kwamishinan kuɗi ya kara da bayanin cewa gwamnatin Ortom ta nuna wa Gwamna Alia asusu 25 ne kacal lokacin da ya karɓi ragamar mulki a watan Mayu.
Amma a cewarsa, bayanai daga hukumar kula da mu’amalar bankuna ta tarayya ya nuna gwamnatin Benuwai na da asusu sama da 600.
A jawabinsa ya ce:
“Lokacin da muka zo, mun nemi a bamu bayanan asusun banki kuma an gabatar mana da asusu 25. Da muka duba tsarin kula da mu’amalolin banki ya nuna jihar Benuwai tana da asusu sama da 600.”
“Saboda haka ne gwamna ya ga ya kamata a rufe dukkan waɗan nan asusu domin gano me ke faruwa.”
Oglegba ya jaddada cewa gwamnatin Alia ta gaji bashin N359bn wanda ya ƙunshi basukan da ake bin ƙananan hukumomin jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro