Yadda Budurwa ta Hallaka Saurayinta Har Lahira a Jihar Nasarawa
Wata yarinya ta hallaka saurayinta a bayan dakin Otal cikin dare a jihar Nasarawa ranar Laraba.
Yarinyar ta aikata wannan aika-aika ne sakamakon rashin jituwa da ya auku tsakanin masoyan.
An garzaya da ita babban birnin jihar Lafia domin gudanar da bincike mai zurfi da kuma hukunci.
Lafia – Jami’an yan sanda a jihar Nasarawa sun damke wata budurwa mai suna Alice Mulak kan laifin kashe saurayinta a unguwar Mararaba dake karamar hukumar Karu ta jihar.
AIT ta ruwaito cewa Alice Mulak ta kashe saurayin ne yayinda fada ya kaure tsakaninsu.
Read Also:
Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa abin ya auku ne ranar Laraba a bayan dakin Otal na City Rock Hotel.
Ya kara da cewa tuni yarinyar ta shiga hannu kuma an gano wukan da tayi amfani da shi wajen aikata kisan.
A jawabin da ya fitar yace:
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wannan ab ya faru ne bayan City Rock Hotel.Mararaba misalin karfe 0330hrs lokacin da mamacin da budurwarsa suke samu sabani.”
“An kamata da wukan da tayi amfani da shi bisa umurnin kwamishanan yan sanda, CP Adesina Soyemi.” “An garzaya da ita sashen CID Lafia don cigaba da bincike da hukunci.”