Shugaba Buhari ya Bayyana Cewa Hutawa Yake a Landan

 

Makon shugaba Buhari daya yanzu a birnin Landan.

Sabanin abinda hadimansa suka fada na cewa ya tafi jinya, Buhari ya ce hutawa ya tafi yi.

Hakan ya janyo cece-kuce a kafafen ra’ayi da sada zumunta Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana dan hutawa ne a Landan, kasar Birtaniya.

Buhari ya bayyana hakan ne a wasika ta musamman da ya aike ga Sarkin Urdu, Abdullah ll Bin Al-Hussein, kan rikicin da masarautarsa tayi fama da shi kwanakin baya.

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki mai taken:

“Shugaba Buhari ya aike wasika ga Sarkin Urdu Abdullah, yana masa fatan Alheri.”

A cewar Garba Shehu, Buhari ya yi matukar damuwa lokacin da ya samu labarin abubuwan da ke faruwa a masarautar kadar amma ya ji dadin samun labarin cewa komai ya yi daidai yanzu.

Ya ruwaito Buhari da cewa: “Yayinda nike Landan ina dan hutawa, na yi matukar damuwa kan labarin da na samu cewa wasu na kokarin tayar da tarzoma a masarautar Urdu.”

“Amma mutuncinka da iya shugabancinka ya janyo hankalin kasashen duniya gaba daya.”

“Mai martaba, ina farin ciki an sassauta abubuwa yanzu kuma ina addu’a masarautar Hashimiya za ta cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya da lumana.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here