Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Gagararen Shugaban ‘Yan Boko Haram, Alhaji Modu da ‘Yan Ta’adda 27

 

Zakakuran dakarun sojin Najeriya sun halaka Alhaji Modu, gagararen shugaban ‘yan ta’addan Boko Haram da wasu 27.

Wannan ya biyo bayan luguden wutan da sojin saman Najeriya suka yi a tsaunikan Mandara dake karamar hukumar Gwoza ta Borno.

Kamar yadda aka gano, sojin saman sun yi luguden ne sakamakon bayanai da suka same su na cewa ‘yan ta’addan suna shirya kai famaki.

Dakarun sojin saman Najeriya karkashin Operation Hadin Kai sun bayyana halaka fitaccen shugaban ‘yan ta’addan Boko Haram, Alhaji Modu.

Kamar yadda Zagazola Makama, kwararre wurin yaki da ta’addanci ya tabbatar, Modu wanda aka fi sani da Bem Bem an halaka shi tare da wasu mayakan ta’addanci 27 a Borno.

Yace an halaka Modu a ranar 3 ga watan Augustan 2022 a luguden wuta da sojin sama suka kai tsaunikan Mandara dake karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

“Bayan luguden wutan, binciken da aka yi a wurin ta jiragen sama ya bayyana yadda aka ragargaza tare da halaka ‘yan ta’addan, yayin da aka raunata wasu masu yawa,” majiyar tace.

Kamar yadda yace, majiyar tace an kai samamen ne bayan bayanan sirri da aka samu kan cewa mayakan ISWAP suna tattaruwa da yawansu domin aiwatar da wasu farmaki.

“BemBem fitaccen mai safarar kawayoyi ne wanda ya fara da fashi da makami zuwa shugaban ‘yan Boko Haram. Yana daga cikin ‘yan ta’addan da suka tada garin Bama a 2014 inda suka halaka daruruwan mutane tare da kafa daularsu,” Makama yace.

Ya kara da cewa, Modu ya dade yana boyewa a kogunan tsaunin Mandaa inda yake hada farmakin da ake kai wa Najeriya, Kamaru da Nijar, The Cable ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here