Shin da Gaske ‘Dan Shugaban INEC ya Kamu da Hauka ?

 

Wani ikirari da ba a tabbatar ba ya bayyana a soshiyal midiya kan iyalan Mahmood Yakubu, shugaban INEC, bayan babban zaben Najeriya na 2023.

Daya daga cikin ikirarin da aka yi a soshiyal midiya ya yi zargin cewa dan Yakubu ya haukace a kasar Saudiyya saboda ta’ammali da miyagun kwayoyi da shan barasa.

Sai dai, Africa Check ya binciki lamarin sannan ya gano babu wata hujja da ke tabbatar da hakan, kuma cewa kakakin Yakubu ya bayyana lamarin da “labaran karya”.

Bayan gudanar da babban zaben 2023 a Najeriya, an yi wani ikirari mara tabbass a kan iyalan Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe na kasa mai zaman kansa (INEC) a soshiyal midiya.

Wani rubutun Facebook da ke yawo a Najeriya a watan Mayun 2023 ya yi zargin cewa dan Yakubu ya haukace a kasar Saudiyya.

Rubutun na dauke da shafin labarin da ya alakanta lamarin ga miyagun kwayoyi da shan barasa. Shafin labarin na Facebook ya nakalto wani gidan jarida na kasar Saudiyya a matsayin majiyarsa.

Bugu da kari, labarin ya yi zargin cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta bukaci shugaban INEC da ya dauki dansa zuwa Ingila don yin magani.

Sai dai kuma, an yi ikirarin cewa iyalan Yakubu sun gaza nemawa dansu magani a UK da US saboda haramcin da aka sanya masa kan zargin rawar ganin da ya taka wajen kawo karan tsaye ga zaben 2023.

Ikirarin da aka yi dangane da dan Yakubu da kuma zargin rashin lafiyarsa ya bayyana a wasu majiyoyi, ciki harda nan da nan.

Menene gaskiyar ikirarin cewa dan shugaban INEC ya haukace?

Africa Check, wani hukumar binciken kwakkwafi, ya binciki sahihanci ikirarin.

A cewar hukumar, kakakin Yakubu, Rotimi Oyekanmi, ya bayyana ikirarin a matsayin “labarin karya” sannan ya bukaci masu karatu da su yi watsi da shi.

A cewar babban sakataren labaran na Yakubu, bayani daga labarin bai da tushe.

“Ikirarin “labarin kanzon kurege ne, dan Allah ku yi watsi da shi”, inji Oyekanmi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here