Zan Saka Kafar Wando ɗaya da Duk Wani Dake Kokarin Dawo da Hannun Agogo Baya a Jahata – Gwamnan Jahar Plateau

 

Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong, yace sam ba zai lamurci duk wani yunkuri na tada zaune tsaye a jaharsa ba.

Gwamnan ya faɗi haka ne bayan ya kai ziyarar duba wasu daga cikin waɗanda lamarin Jos ya shafa.

Lalong yace lokaci ya yi da zai sa kafar wando ɗaya da duk wani dake kokarin dawo da hannun agogo baya a jaharsa.

Plateau – Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong, yace ba zai lamunci duk wani yunkuri na tada rikici a jaharsa ba ta hanyar yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Aƙalla matafiya 22 aka kashe a wani hari da aka kai kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta rewa, jahar Filato.

Harin, wanda aka kaiwa wasu jerin motocin Bas dake ɗauke da mabiya addinin musulunci dake kan hanyarsu ta komowa Ondo bayan halartar wa’azi a Bauchi, ya bar wasu mutum 14 cikin rauni.

Lalong yakai ziyara ga mutanen da abun ya shafa

Da yake jawabi bayan ziyarar da yakai wa wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Lalong yace gwamnati zata cafke tare da hukunta kowaye ta samu da yaɗa labaran karya da ka iya tada wutar rikici.

Gwamna Lalong yace:

“Ba zamu bari a tada rikicin addinai ba, mutane su dakatar da yaɗa labaran da basu da asali, irin wannan kisan na faruwa ne ta sanadiyyar haka.”

“Ina tabbatar muku zamu sa kafar wando ɗaya da mutanen dake yaɗa sakonnin karya waɗanda ke jawo ana hallaka mutanen da ba su ji ba basu gani ba.”

“Wannan gargaɗi ne kai tsaye ga duk wanda keson dawo mana da abinda muka mance da shi. Lokaci ya yi da zamu ɗauki mataki kan waɗannan mutanen duk mukaminsu.”

Gwamnan ya kara da cewa ya kai wannan ziyarar ne domin duba yadda mutane ke ɗa’a ga dokar zaman gida da gwamnatinsa ta sa a yankin.

Zuwa yanzin rundunar sojin Operation Safe Haven ta kame mutum 12 da ake zargin suna da hannu a kisan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here