Zambar Intanet: Hukumar EFCC ta Kama Matashi Mai Dalilin Auren Bogi
Hukumar hana yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta kama wani matashi da abokansa bisa laifin zamba.
Haka kuma ana zargin matashi Audu Ishida da bude shafukan bogi da ke hada masoya inda ta nan ne ya ke cin kudin jama’a.
Yanzu haka babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna na sauraron tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ta shigar gabanta.
Jihar Kaduna – Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa ta kama wani matashi mai dalilin aure na bogi.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta kama matashi, Audu Ishida da aka fi sani da Baddie Kylemili a bisa zargin damfara ta kafar intanet.
Read Also:
Hukumar ta wallafa a shafinta na X cewa ana zargin matashin da yin sojan gona, samun kudin haramun da kuma halasta kudin haram.
An kama matashin tare da wasu abokan huldarsa da su ka kware wajen damfara ta kafar intanet a Jos.
EFCC ta gurfanar da matashi kotu Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce ta gurfanar da matashin da ake zargi da aika laifuffuka ta intanet gaban kotu, Jaridar Leadership ta wallafa.
Yanzu haka babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ce ke sauraron shari’ar matashi Audu Ishida karkashin jagorancin mai shari’a, Hauwa’u Buhari.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa an gano yadda Ishida ya bude shafukan sada zumunta da ke hada masoya, kuma ta nan ya ke damfarar jama’a.
An kuma bankado yadda ya rika samun kudi ta hanyar kafar inda ya ke musanya kyautar kudaden da ake ba shi zuwa Naira.