Kuna Gab da Fara Kallona a Cikin Fina-Finan Bollywood – Rahama Sadau ga Masoyanta

 

Jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau ta ce tana shirin bayyana a fina-finan Bollywood na Indiya.

Rahama ta bayyana cewa tuni suka zanta da Furodusa kuma Daraktar shirin, Hamisha Daryani Ahuja, wacce ta yi mata tayin shiga sabon fim dinta.

Ta mika godiya ga dukka masoyanta a kan goyon baya da irin gudunmawar da suke bata wanda ya kai ta ga hawa wannan mataki.

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau ta ce ta yiwa masoyanta albishir da cewar suna gab da fara kallonta a cikin fina-finan kasar Indiya wato Bollywood.

A wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram, Rahama ta bayyana cewa ta cika farin ciki bayan samun kira daga Furodusa kuma Daraktar shirin , Hamisha Daryani Ahuja cewa tana son ta fito a wani sabon fim dinta.

Hakazalika, jarumar ta kuma wallafa wani bidiyonta tana zuba yaren Indiyanci tiryan-tiryan sai kace Ba’indiyar usuli.

Ta rubuta a shafin nata:

“Na girma da kallon fina-finan Bollywood, kuma har na kan hango kaina cikin shirin a matsayin jaruma. A koda yaushe ina jin dadin yadda al’adar Indiya ke shige da al’adar da na girma a ciki.

“A lokacin da @hamishadaryaniahuja da ni muka yi magana game da yiwuwar aiki kan shirinta mai zuwa, na cika da farin ciki. Na san cewa rawar gani ne da za ta mikar da ni, sannan zai nuna kwarewata a matsayin jaruma, kuma ina zuba idon ganin abun al’ajabin da hakan zai haifar!

“Abu mafi muhimmanci, ina dokin sanar da ku dukka da kuka kamaramun baya duk daga ranar farko yadda za ta kasance. Na iya yin duk wadannan abubuwan ne, saboda kuna tare da ni.”

 

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here