Guguwa ta yi Sanadin Mutuwar Mutane 14 a Madagascar da Mozambique

 

Akalla mutum 14 ne suka mutu, bakwai a Madagascar, bakwai kuma a Mozambique sakamakon wata mahaukaciyar guguwa.

Haka kuma adadin mutanen da guguwar Freddy ta shafa ya ƙaru zuwa 383,000 a Madagascar da fiye da 163,300 a Mozambique, a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

“Ko da yake tsananin guguwar bai kai yadda muke zato ba, dubban ɗaruruwan mutane suna bukatar agajin jin kai. Za a ɗauki watanni kafin a farfado,” in ji Pasqualina Di Sirio, wakiliyar hukumar samar da abinci ta duniya a Madagascar.

Ba zai yi wu a samu ambaliya a kudu maso gabashin Zimbabwe ba saboda mahaukaciyar guguwar ba ta kai cikin kasa kamar yadda aka yi hasashe a baya ba.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here