Indiya ta Haramta Sayarwa da Raba Nama na Tsawan Kwana Tara

 

Hukumomi a birnin Ayodhya na Indiya sun haramta sayarwa da rabawa da adana nama da duk wani abu da ya shafi nama har tsawon kwana tara na bikin addinin Hindu.

Sun ce haramcin zai fara ne daga ranar Alhamis da za a soma bikin kuma ya shafi masaukin baƙi da gidajen sayar da abinci.

Mahukunta birnin da ke jihar Utter Uttar Pradesh sun yi gargaɗi ga ƴankasuwa cewa za su fuskanci fushin hukuma idan har suka saɓa umarnin.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da kuma musulmi tsiraru sun soki matakin na haramcin nama a bikin Hindun na Navaratri.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here