INEC ta Dakatar da Kwamishinan Zabe na Jihar Sokoto

 

INEC ta dakatar da kwamishinanta na jihar Sakkwato kuma nan take ta maye gurbinsa.

A wata wasiƙa da ta tura zuwa reshenta na jihar, INEC ta umarci Nura Ali ya miƙa komai hannun Sakatariyar gudanarwa.

Wani ma’aikaci ya bayyana cewa jinkirin da aka fuskanta a zaben da ya gabata ne suka haddasa ɗaukar wannan matakin.

Abuja – Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dakatar da kwamishinan zabe a jihar Sakkwato (REC), Dakta Nura Ali, kuma matakin zai fara aiki nan take.

Channels tv ta ce hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakataren INEC, Rose Orlaran-Anthony, zuwa ga REC ɗin da Sakataren hukumar na jihar.

Wasiƙar ta umarci Dakta Ali ya tattara ya bar Oishin hukumar INEC da ke jihar Sakkwato, arewa maso yammacin Najeriya, har sai baba ta gani.

Haka nan INEC ta umarci Sakatariyar gudanarwa, Hajiya Aliyu Kangiwa, ta maye gurbinsa nan take.

Wannan na zuwa ne awanni 48 bayan shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya lashi takobin gano jami’an hukumar masu sakaci da ɗaukar mataki kansu, sai ga shi ya cika kalamansa a aikace.

Meyasa INEC ta dakatar da REC na Sakkwato?

Duk da wasiƙar ba ta ambaci dalilin ɗaukar mataki kan REC ɗin ba, amma wata majiya a INEC ta shaida wa Daily Trust cewa yana da alaƙa da abinda wasu ma’ikatan karkashin Ali suka yi a zaben da ya gabata.

Legit.ng ta tattaro zaben da ya gudana a Sakkwato cike yake da matsaloli da jinkiri, idan aka jingine na shugaban kasa wanda PDP ta samu nasara, sauran an ce ba su kammalu ba har da na Sanatoci uku.

Wannan ne karo na farko da Nura Ali ya jagoranci zaɓe tun bayan naɗa shi a matsayin kwamishina a shekarar da ta gabata.

Yayin da yake tsokaci kan ci gaban, majiyar ta ce:

“Kun san an samu jinkiri da dama a zaben da ya gabata, rashin zuwan kayan zaɓe rumfunan kaɗa kuri’a da wuri da rashin baiwa ma’aikatan wucin gadi horo mai kyau.”

“Kuma jihar Sakkwato na da wuyar sha’ani a batun zaɓe, tana bukatar gogagge, mai kwarewa. Ruɗanin da ya faru lokacin zaben baya ne babban makasudin dakatar da shi.”

“Yanzu an turo tawagar kwararru kuma gogaggu da zasu jagoranci zaben gwamna da sauran zaɓukan da ke tafe a jihar.”

Wani babban jami’in INEC da ya nemi a boye sunansa domin ba shi da hurumin magana kan batun, ya ce baki ɗaya ma’aikata a jihar sun bar Nura Ali shi ɗaya saboda salon jagorancinsa.

“INEC ta fahimci cewa REC ɗin Sokoto na aiki kamar shi kaɗai ne mai gudanarwa hakan ya jawo rushewar tsarin gudanarwa na hukumar a Sakkwato.”

“Alal misali, har yanzu babu sakamakon zaben majalisar tarayya ko ɗaya daga jihar sakamakon ma’aikatan sun ƙaurace masa saboda ya riƙe komai,” inji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here