Gwamnatin Jihar Jigawa da Sokoto Sun Rage Lokutan Aiki Saboda Ramadan
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki a jihar da sa’o’i biyu ga ma’aikatan gwamnatin jihar a cikin watan Ramadan.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri.
Sanarwar ta ce a yanzu ma’aikatan za su fara aiki da ƙarfe 9 na safe kuma za su kammala da ƙarfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis sabanin ƙarfe 5 na yamma da aka saba rufewa.
A ranar Juma’a kuma, ma’aikata za su fara da ƙarfe 9 na safe kuma za su rufe da ƙarfe 1 na rana kamar yadda aka tsara.
Read Also:
Kazalika a jihar Sokoto, gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, shima ya amince da rage sa’o’in aikin ma’aikatan gwamnati saboda azumi.
Abubakar Bawa, sakataren yaɗa labarai na Gwamnan jihar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa.
Ya ce ma’aikata a jihar za su kammala aiki da karfe 2:30 a maimakon 4:00 daga ranar Litinin zuwa Alhamis, inda kuma a ranar Juma’a, za su rufe aiki da karfe 12 na rana.
Jihohin biyu sun ce hakan na da nufin bai wa ma’aikatan isasshen lokaci don yin shirin buɗe baki na azumi tare da ba da damar haɓaka ayyukan ibada a cikin wannan wata mai alfarma.
Jihohin sun kuma shawarci ma’aikatan da za su yi amfani da lokacin azumin watan Ramadan wajen yi wa jihohin biyu addu’ar zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da ma Najeriya baki daya”.