Jirgin Sama ya Maƙale a Karkashin Gada a Birnin Delhi

 

Wani hoton bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta kan yadda wani jirgin sama ya makale a karkashin gada a birnin Delhi.

Lalataccen jirgin wanda rahotanni ke cewa an sayar, ana kan hanyar jansa lokacin da ya maƙale.

Hoton bidiyon ya nuna yadda motoci suka rinƙa ratsa gefen jirgin da ke maƙale.

Wani ɗan jarida wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na twitter, ya wallafa sanarwar da Air India ta fitar da ke cewa ba ta da alaƙa da jirgin.

Mahukunta filin jirgin saman Delhi sun shaidawa jaridar Times of India cewa, jirgin ba shi da alaƙa da filin jirgin saman Delhi, sannan ta kara da cewa babu mamaki direban ya yi kuskure ne lokacin jan jirgin.

Dubban mutane ne suka kalli bidiyon a shafukan Twitter da Youtube, yayinda mutane ke tambayar garin ya ya jirgin ya maƙale.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here