Kano ta Shiga Jerin Jihohi 16 da Suka Amince da Biyan Albashi Mafi ƙanƙanta 

 

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta daddale naira 71,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta da za ta biya ma’aikatanta.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatin jihar ranar Talata bayan ganawa da wakilan ƙungiyar ƙwadago.

Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ta ce ƙarin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.

Kano ta zama ɗaya daga cikin jihohin da suka amince da biyan sama da abin da gwamnatin tarayya ta amince na N70,000 tun a watan Yuli.

Jihohin Legas da Rivers ne kan gaba bayan sun amince da N85,000, sai kuma Neja da ta ce za ta biya N80,000.

Jihohin Najeriya da suka amince da biyan albashi mafi ƙanƙanta na N70,000 ko fiye

A watan Yulin 2024 ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa 70,000.

Sai dai kuma aiwatar da shi ya zama jidali a faɗin jihohin ƙasar, inda har yanzu wasu ba su kama hanyar biya ba.

A gefe guda kuma, yayin da wasu jihohin suka amince da biyan N70,000 ɗin, wasu kuma sun ci alwashin biyan sama da hakan.

Wannan maƙala ta yi duba kan jihohin da suka amince da N70,000, da waɗanda suka ce za su biya sama da hakan.

Jihohin da za su biya sama da N70,000

Legas

A ranar 16 ga watan Oktoban 2024 Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da sabon albashin mafi ƙanƙanta, inda ya ce za su fara biyan N85,000.

Hakan na nufin ƙarin naira 15,000 kan abin da gwamnatin tarayya ta ƙayyade.

Kazalika gwamnan ya ce yana fatan gwamnatinsa za ta ƙara albashin zuwa N100,000 nan da watan Janairun 2025 “saboda tsadar rayuwar da ake ciki”.

Rivers

Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ma ya sanar da N85,000 a matsayin albashin mafi ƙanƙanta da za su biya ma’aikata a jihar.

Ya sanar da hakan ne a ranar 18 ga watan Oktoba.

Neja

Gwamnatin jihar neja da ke arewacin ƙasar ta sanar da amincewa da biyan N80,000 ga ma’aikatan jihar, kamar yadda Gwamana Mohammed Umaru Bago ya sanar a shafinsa na zumunta ranar 25 ga watan Oktoba.

Ogun

Gwamna Dapo Abiodun ma na jihar Ogun ya amince da biyan N77,000, kamar yadda wata sanarwa daga sakataren gwamnatin jihar ta nuna a ranar 15 ga watan Oktoba.

Kebbi

A ranar 23 ga watan Oktoba kuma, Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya sanar da amincewa da N75,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Gombe

A jihar Gombe kuwa, gwamnati da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago sun saka hannu kan yarjejeniya ranar 14 ga watan Oktoba da zimmar ɗaga albashin mafi ƙanƙanta zuwa N71,451.

Ondo

Jihar Ondo ma ta bi sawun takwarorin nata, inda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya sanar da N73,000 da za a biya ma’aikatan jihar a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.

Sanarwar tasa ta zo ne yayin da ake shirin gudanar da zaɓen gwamnan jihar ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kogi

Gwamnan Kogi Usman Ododo ya amince da biyan N72,500 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi a jihar.

Haka nan, wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook ta ce gwamnatin ta soke biyan haraji a kan sabon albashin na shekara ɗaya.

Kano

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta daddale naira 71,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta da za ta biya ma’aikatanta.

Bayan ganawa da wakilan ƙungiyar ƙwadago ranar Talata 29 ga watan Oktoba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ƙarin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.

Jihohin da za su biya N70,000

Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa gwamnati za ta fara biyan N70,000 daga watann Oktoban 2024.

A ranar 25 ga watan Oktoba Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya sanar da amincewa da N70,000 a gidan gwamnati jim kaɗan bayan ya karɓi rahoton kwamatin da ya kafa kan mafi ƙanƙantar albashin.

Shi ma Gwamnan Katsina Dikko Radda ya ce gwamnatinsa na shirin fara biyan N70,000 ɗin.

Tun a watan Satumba ne kuma gwamnatin Ebonyi ƙarƙashin jagorancin Francis Nwifuru ta amince da biyan N70,000 ga ma’aikatan jihar.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, na cikin na farko-farko da suka sanar da amincewa da N70.000 tun a watan Agusta – wata ɗaya bayan saka wa sabuwar dokar hannu.

Shi ma Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara biyan N70,000 da zarar an daddale maganar ƙarin albashin baki ɗaya.

Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta fara biyan N70,000 daga watan Oktoban 2024.

Su ma jihohin Osun da Binuwai sun bayyana aniyarsu ta fara biyan sabon albashin mafi ƙanƙanta.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, jihohin da ba su kai ga cim ma matsaya ba game da biyan N70,000 ko sama da haka sun ƙunshi Zamfara, da Akwa Ibom, da Bayelsa.

 

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here