Na Kasance Talakar Karshe ta Yadda Har Sai na Roki Makwabta na Abinci – Jarumar Fim

 

Jarumar fim, Bisola Aiyeola ta magantu game da wani bangare na rayuwarta da mutane da dama basu sani ba.

A cikin wani sabon bidiyo da ya bayyana, jarumar ta bayyana cewa babu wani lada da ake baiwa mutanen da suka sha wahala a rayuwa.

Bisola ta magantu game da irin talauci na gidansu yayin da ta bayyana cewa babu laifi don sun kashewa jikinsu a lokacin da suke da halin yin hakan.

Jarumar masana’antar shirya fina-finan kudu kuma tsohuwar yar gidan BBNaija, Bisola Aiyeola ta haddasa cece-kuce a tsakanin mutane da dama bayan ta magantu game da irin rayuwar da ta yi a baya.

Jarumar a cikin wani bidiyo da ya yadu ta bayyana yadda mutane suka cancanci duk wani abu da rayuwa ta kawo masu sannan cewa su karbi abun alkhairin da zai tunkaro su da hannu bibbiyu.

Bisola ta bayyana cewa babu wata kyauta ta musamman ga mutumin da ya wahala yayin da ta sanar da mutane irin wahalar da ta sha a baya a rayuwarta.

A cewarta abun ya yi muni a wancan lokacin ta yadda sai ta jira makwabtanta sun kammala girki kafin ta samu abincin da za ta ci.

Sai dai kuma, jarumar ta kara da cewar ta kuma dandani dadin rayuwa kuma ta fahimci cewa babu wata karramawa da ake yiwa mutanen da suka fi kowa shan wahala.

Ta karfafawa mutane gwiwar jin dadin rayuwarsu idan har suna da halin yin hakanA cewarta, mutane na iya daukaka abubuwan jin dadin rayuwa, musamman idan sun yi aiki tukuru ta yadda za su iya daukar nauyin jin dadi na musamman.

Jama’a sun yi martani

callmeanilanry_dmw ya ce:

“Kowa na fuskantar matsaloli da dama.”

itz_abi_young_ ya ce:

“Talauci bai da kyau ko kadan. Babu abun da ke da dadi kamar ka mallaki kudi.”

queeen__oma ta ce:

“Haka nake kashe kudina da dukkan jikina.”

faustinadung ya ce:

“Yan Najeriya basa son jin irin wannan sai dai baka kai ni shan wahala ba muka iya.”

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here