Kano: An Kashe Mutum ɗaya Yayin Wawaso a Rumbun Abinci na Hajiya Mariya 

 

 

Rahotonni daga jihar Kano na cewa an kashe mutum ɗaya yayin da wasu ɓata-gari suka fasa wurin ajiyar kayan abinci mallakar Hajiya Mariya Sanusi mahaifiyar Aliko Dangote.

Wani da ya shaida lamarin ya bayyana cewa masu wawason sun kwashe kayan abinci da dama kafin ‘yansanda su ƙarasa wurin, inda suka kwashe sauran abin da ya rage.

“Yanzun nan muka dawo daga maƙabarta, sun kashe ɗan yayarmu a wurin,” kamar yadda wani da ya shaida yadda abin ya faru ya faɗa wa BBC.

Lamarin ya faru ne a unguwar Koki da ke cikin ƙaramar hukumar Birni, wurin da Mariya Sanusi ke da wuraren ajiyar kayan abinci da ake girkawa domin tallafa wa marasa ƙarfi a faɗin jihar ta Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here