An Kashe ƴan ci-rani 6 da Jikkata 10 a Mexico

 

Ma’aikatar tsaro a Mexico ta ce an kashe mutum shida da jikkata 10 lokacin da sojoji suka buɗe wuta a kan motar da ta ɗauko ƴan ci-rani.

Ma’aikatar ta kuma ce motar ta yi ƙoƙarin kutsa kai shingen bincike na sojoji a jihar Chiapas da ke kudancin ƙasar.

Ma’aikatar ta ce motar na ɗauke ne da baƙin-haure 33 daga ƙasashen Masar, Nepal, Cuba, Indiya da kuma Pakistan, “kuma ana ta rafka gudu da su, kamar an kwaso ɓarayi, sannan sai jami’an tsaro suka ji kamar ƙarar fashewar abu, wanda hakan ne ya sa suka buɗe wa motar wuta.”

Tuni aka ƙaddamar da bincike a kan lamarin, bayan an sanar da dakatar da sojojin da suka yi harbin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here