Ahmed Musa ya yi Kira ga Gwamnatin Najeriya Kan Kashe Matafiya a Jos
Fiye da mutane 22 suka rasa rayukansu a arewacin Najeriya yayin da suke kan hanya a Jos.
Da dama kuma sun samu munanan raunuka sakamakon tsallake mutuwa da kyar da suka yi.
Fitaccen dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa ya yi kira ga gwamnati da ta tashi ta kawo kariya ga al’umma.
Istanbul, Turkiyya – Fiye da mutane 22 sun rasa rayukansu a arewacin Najeriya yayinda wasu da dama suka samu raunuka sakamakon tsallake mutuwa da kyar da suka yi.
Fitaccen dan kwallon kafa, Ahmed Musa, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da tayi saurin tashi tsaye ta kula da rayuka da dukiyoyin al’umma domin aikinsu ne hakan.
Ahmed Musa ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da tayi gaggawar kawo karshen yadda ‘yan bindiga suke kashe ‘yan Najeriyan da basu ji ba basu gani ba.
Read Also:
Dan kwallon mai shekaru 28 ya yi tsokacin ne a shafinsa na Instagram a kwanakin karshen mako yana bayyana takaicinsa akan kisan da aka yi wa mutane 22 wadanda suke hanyarsu daga Bauchi daga wani taron addini.
Rahotonni sun bayyana yadda wasu daga cikin matafiyan suka samu miyagun raunuka sakamakon mummunan hatsarin da suka samu a arewacin kasar nan sakamakon harin da aka kai musu a titin Rukuba dake karamar hukumar Jos ta arewa dake jahar Filato.
Kamar yadda Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na Instagram:
Kashe-kashe da aka yi wa matafiyan nan da suka taho daga Bauchi bayan sun kammala zikirin sabuwar shekarar musulunci suna hanyar komawa gidajensu yayin da aka kai musu farmaki a titin Rukuba na Jos ta arewa abin takaici ne.
Ina kira ga gwamnati da duk wasu hukumomi da ya kamata su samar da tsaro a kasar nan da su yi gaggawar kawo dauki don hana irin wannan lamari faruwa. Muna musu fatan rahama kuma Ubangiji ya samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jaharmu da Najeriya baki daya.