Dalilin da Yasa Malamai ba sa Iya Fadawa Shugabanni Gaskiya – Sheikh Gumi

 

Sheikh Ahmad Gumi ya ce a daina ganin laifin Malamai, yan siyasa suka lalatasu.

Babban Malamin yace wani malamin ba zai kwana gidansa ba idan yayi wani magana.

Malam Gumi ya kasance mai rajin ganin karshen matsalar yan bindiga.

Kaduna – Shehin Malamin addinin Islam, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya yi Alla-wadai da yadda yan siyasa sukayi tururuwa zuwa daurin auren ‘dan Buhari da Zahra Bayero.

Babban Malamin ya yi Alla-wadai kan yadda yan siyasa suka yi amfani da dukiyar al’umma wajen baja koli da hayar jiragen alfarma.

Malamin ya yi bayyana dalilin da yasa Malamai ba sa iya fadawa shugabanni gaskiya.

Yace duk yan siyasa sun lalata Malaman addini shiyasa basu iya musu wa’azi, su fada musu gaskiya.

Gumi ya bayyana hakan yayin karatun Tafisrin mako-mako da yake gudanarwa a Masallacin Sultan Bello dake jahar Kaduna.

Yace:

“Kar ku ba Malamai laifi, domin wani Malamin ba zai iya rayuwa sai yayi dan amshin shata saboda yunwa. Wani Malami in yayi wata magana ba zai kwana gidansa ba, cikinCell zai kwana. In kuma an nemeshi zaku je ku fito da shi? Dole yayi shiru.”

“Shiyasa Yan siyasa suka lalata mana Malamai. ana barna cikin kasa ba mai wa’azi, ba mai gaya musu gaskiya. Sannan barnan nan babu inda za ta kaimu sai ga wahala.”

“Ga kuna barnar kudi jirgae kuke dauka zuwa aure, sannan ga wasu mabarnata a daji suka tatse mutane.” Mutane sun tsamannin wadanda ke daji ke tastanmu, har shugabanninmu suna tatsanmu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here