Tunda Yanzu Mahaifina ya Rasu, Yanzu Bani da Baba Sai Obasanjo – Gwamna Dapo Abiodun

 

Gwamnan jahar Ogun ya bayyana wata magana mai nauyi ga tsohon shugaban kasar Najeriya.

A cewar gwamnan, tunda yanzu mahaifinsa ya rasu, yanzu ba shi da baba sai dai Obasanjo.

Ya bayyana haka ne yayin da tsohon shugaban kasar na Najeriya, Obasanjo ya je masa jaje.

Ogun – A wani lamari mai ban mamaki, gwamnan jahar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya sanar da canza sunan mahaifinsa kwanaki bayan rasuwar mahaifin nasa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa.

Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Abiodun ya ce Obasanjo ya kasance mahaifinsa tsawon shekaru tun kafin ma mahaifin nasa ya kwanta-dama, ya kara da cewa dole ne tsohon shugaban ya tsaya masa a yanzu a matsayin mahaifinsa.

A cewarsa:”Baba, ba inda za ka. Baba, cikin ikon Allah, za ka kara tsawon rai. Ba za mu iya jurewa ba ka tafi yanzu.

Ka kasance mahaifina tsawon shekaru, amma, yanzu mahaifina na haihuwa ya tafi ya sadu da tsarkakanasa, dole ne ka tsaya yanzu don zama mahaifina.”

Ya roki Obasanjo da ya dauki nauyinsa a matsayin mahaifinsa tunda mahaifinsa ya mutu, ya kara da cewa tunda tsohon shugaban bai yi watsi da bukatar ba, ana iya aminta da cewa ya amince da shi nan take.

Kamar yadda rahoton ya nuna, gwamnan ya samu nasarar ‘shiga’ ga dangin Obasanjo, daga asalin sa na Abiodun.

A martaninsa, Obasanjo ya ce mahaifin gwamnan, Pa Abiodun ya mutu cikin salama, ya kara da cewa tsawon shekara 89 na rayuwarsa, babu wanda ya taba zarginsa da aikata miyagun ayyuka.

Ya ce rayuwa mai tsawo a irin wannan lokaci a cikin wannan yanayi na bakin ciki a cikin kasar da Allah ya ba ta kyakkyawar hula amma babu kai da zai sa ta, babban aiki ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here