‘Yan Sanda Sun Kama Matashi Dauke da Bindigogi 53 a Jahar Nasarawa

 

‘Yan sanda sun cafke wani matashi a lokacin da yake safarar bindigogi kirar AK-47 guda 53 a jahar Nasarawa.

Har ila yau, an kuma gano albarusai akalla guda 260 a wurin mutumin da ya shiga hannu a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta.

Matashin ya shiga hannu ne a hanyarsa ta safarar makaman zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Nasarawa – Rundunar ‘yan sandan jahar Nasarawa ta cafke wani mutum mai suna Likita Abubakar da makamai.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an cafke Likita mai shekara 35 dauke da bindigogi 53 kirar AK-47 da harsasai 260, a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta.

An tattaro cewa yana shirin kai makaman zuwa wani waje da ba a sani ba a cikin jahar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jiahar, ASP Ramhan Nansel, ya shaida wa Aminiya cewa an cafke wanda ake zargin ne a karamar hukumar Akwanga da ke jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here