Zuwan Mbappe Real Madrid ba Zai Canza Matsayin Bellingham ba – Ancelotti

 

Matsayin Jude Bellingham a Real Madrid ba zai canza ba a bana, bayan ɗaukar Kylian Mbappe, in ji Carlo Ancelotti.

Bellingham ɗan wasan Ingila, mai shekara 21, ya taka rawar gani a Sifaniya a kakarsa ta farko, wanda ya zura kwallo 23 a wasa 42.

Yana cikin ƴan wasan da suka taka rawar gani a Real Madrid, wadda ta lashe La Liga da Champions League a kakar da ta wuce.

Mbappe, kyaftin ɗin tawagar Faransa, mai shekara 25, ya koma Real Madrid a bana daga Paris St Germain, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a watan Yuni.

Ancelotti ya yi watsi da batun cewa Bellingham ba zai ke buga gurbin da ya saba a Real Madrid ba, domin bai wa Mbappe dama, ya kara da cewar: “Babu wani abu da zai canza a gare shi.

“Kakar farko, ya bai wa mutane mamaki, saboda yadda ya nuna ƙwarewa, yanzu kuma ya kara samun gogewa. Kenan wannan kakar haka zai ci gaba da taka rawar gani.

”Zai ci gaba da zama fitatcen ɗan wasan Real, wanda zai ci gaba da taka rawar da ƙungiyar za ta ci gaba da samun nasarori.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here