Harin Jirgi Maras Matuƙi : An Tabbatar da Mutuwar Mutane 85 a Kaduna

 

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kaduna ta ce aƙalla mutum 85 ne, kawo yanzu, aka tabbatar sun mutu a harin da aka kai jihar.

Hukumar ta samu bayanai daga hukumomin yankin cewa tuni aka yi jana’izar mutanen da suka rasu, ana kuma ci gaba da yin bincike.

Tun farko dai rundunar sojin saman ƙasar ta musanta hannu a kai harin.

A jiya Litinin ne, Majalisar Dattawan Najeriya ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar sojin kasar ta kai, da ya janyo asarar rayuka.

Harin dai ya faru ne yayin da mutanen ke tsaka da taron Mauludi da suke yi duk shekara.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com