Zanga-Zanga: Najeriya ta Gargaɗi ƴan ƙasarta Masu Shirin Zuwa Birtaniya
Gwamnatin Birtaniya ta gudanar da taron gaggawa inda aka tattauna a kan yadda za a shawo kan hargitsi mai nasaba da kin jinin ƴan ci-rani a sassan ingila da kuma Arewacin Ireland.
Mako guda ke nan da mutane suka kai hari kan masallatai da otal-otal da kuma gidajen da masu neman mafaka ke zama.
Kazalika an balle shaguna da kuma jefa wa ƴansanda duwatsu.
Read Also:
Najeriya dai ta gargadi ƴan kasarta da ke shirin tafiya zuwa Ingila a kan su yi la’akari da abin da zai iya biyo baya.
Zanga -zangar da ake yi a kasar ta biyo bayan kisan da aka yi wa wasu yara mata uku a makon da ya wuce.
Jita-jitar da aka riƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta ta ɗora alhakin kisan yaran kan wani ɗan ci-rani.
An kama mutane fiye da 250.
Mnistan cikin gidan Birtaniya, Yvetter Cooper, ya ce duk mutanen da suka yi tarzoma za su fuskanci fushin hukuma.