Cristiano Ronaldo: Dan Wasan ba Zai Buga Wasan Juventus da Barcelona ba

 

  Cristiano Ronado ba zai buga wasan da Juventus za ta fafata da Barcelona ba a Gasar Champions League saboda gwaji  ya nuna har yanzu yana ɗauke da cutar korona.

  Ronaldo ya soki yadda ake gwajin annobar kuma da ma Juventus ba ta bayyana shi cikin waɗanda za su buga mata wasan ba a daren yau Laraba.

  Ɗan shekara 35 ɗin ya killace kansa tun lokacin da ya kamu da cutar a ranar 13 ga watan Oktoba, an kuma sake gwada shi kafin yau.

  Ya faɗa a shafinsa na sada zumunta cewa “lafiya ƙalau” yake kafin ya caccaki salon gwajin cutar da ake kira PCR.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here