Sarkin Kano ya Naɗa ɗansa a Matsayin Ciroman Jihar

 

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai naɗa ɗansa na farko a matsayin Ciroman Kano.

Mahaifin Muhammad Sanusi II, Ambasada Aminu Sanusi ya taɓa riƙe sarautar, sannan Alhaji Nasiru Ado Bayero ya riƙe sarautar har zuwa lokacin da aka naɗa shi Sarkin Bichi a shekarar 2020.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa za a naɗa Aminu Muhammadu Sanusi, wanda ɗansanda ne tare da wasu mutum tara a ranar Juma’a, 25 ga Nuwamban 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sauran waɗanda za a naɗa su ne Mahmud Aminu Yusufu a matsayin sabon Mai Unguwar Mundubawa; Dr. Abubakar Sanusi Usman Shehu II as Ɗan Galadiman Kano da Alhaji Abubakar Aminu Sanusi (Wambai) a matsayin Ɗan Madami.

Sauran su ne Arch. Ali Muktar a matsayin Sa’in Kano da Sarki Yusuf Bayero a matsayin Ƴan Daka da Abdullahi Idris Bayero a matsayin Fagacin Kano da Ado Abdullahi Aminu a matsayin Kaigaman Kano da Idris Sanusi a matsayin Sarkin Sulluɓawa da Mansur Isa Bayero a matsayin Sarkin Kudu sai Abdullahi Sarki Mohammed a matsayin Sarkin Yamma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here