Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya Bawa Gwamnan Zamfara Sarauta

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya nada gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle sarautar Shettiman Sokoto.

Sarkin Musulmin ya ce ya nada Matawalle sarautar ne don irin gudunmawa da girmama masarautun gargajiya.

A baya ma, masarautar Daura ta nada gwamna Matawalle sarautar Barden Hausa Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III ya naɗa gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle “Shettiman Sakkwato”.

A cikin wasikar da ke ɗauke da sanarwar zuwa ga Gwamna Matawalle, mai ɗauke da sa hannun Sarkin Musulmi, Sultan ya ce ya naɗa masa sarautar ne don mutunci da girmamama masarautun gargajiya.

“Mun gamsu da irin mutunci da girmamawa da kulawa da ka ke bawa masarautun gargajiya da ya inganta alaƙarka da fadar Sarkin Musulmi” a cewar wasikar.

Wasikar ta ƙara da cewa masarautar musulmi ta gamsu da nasarorin Mista Matawalle kan tsaro da ya kawo zaman lafiya a jihar.

Idan za a iya tunawa, masarautar Daura ita ma ta naɗa Gwamna Matawalle sarautar Barden Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here