Tinubu ya sa Hannu Kan Dokar Mafi ƙanƙantar Albashi ta N70,000
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sa hannu kan dokar mafi ƙanƙantar albashi ta naira dubu 70,000.
Matakin ya kawo ƙarshen watannin da aka shafe ana tattaunawa tsakanin hukumomi da ƴan ƙwadago da kuma ɓangaren masu kamfanoni.
Tinubu ya sa hannu kan dokar a fadarsa da ke Abuja kwanaki bayan da majalisar dokokin ƙasar ta miƙa masa ƙudirin.
Read Also:
Mai bai wa shugaban Najeriyar shawara ta musamman kan al’amuran majalisar dattijai, Sanata Basheer Lado ne ya tabbatar da matakin cikin sanarwar da ya fitar a Abuja.
Ya ce sa hannu kan dokar da shugaba Tinubu ya yi na nuna ya cika alƙawarin da ya yi wa ƴan ƙasa.
“A yaƙin zaɓe, Tinubu ya yi alƙawarin inganta rayuwar ma’aikata kuma ya cika alƙawarin” in ji Lado.
Bai tsaya iya nan ba, ya tabbatar cewa an samar da dokar mafi ƙanƙantar albashi da yanzu ya zama dole a yi nazafin mafi ƙankantar albashin duk bayan shekara uku saɓanin shekara biyar.
Matakin dai ya zo ne yayin da wasu al’ummar Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga don nuna takaicinsu kan tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki.