‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 15 a Jahar Sokoto

 

Akalla mutum 15 ne suka mutu a wani hari da yan bindiga suka kai wasu kauyuka biyu a jihar Sokoto dake arewacin Najeriya.

Gwamnan jihar Aminu Tambuwal wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar litinin yace kananan hukumomin Goronyo da Illela wannan harin ya shafa.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, Tambuwal yace an kashe mutanen ne yayin hare-haren da aka kai a ranar Lahadi da kuma safiyar Litinin.

Gwamna Tambuwal ya bayyana haka ne jim kadan gabanin gabatar da kasafin kudin na shekarar 2022 gaban majalisar jihar.

Ya kara da cewa mutum 12 aka kashe a Illela sai kuma mutum uku a Goronyo.

Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwan wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata a hare-haren.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here