Ƴan Bindiga Sun Hallaka Shugaban Jam’iyyar LP a Jihar Benue

 

Jihar Benue – Ƴan bindiga sun hallaka wani shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Benue.

Ƴan bindigan sun hallaka Mista Sunday Oche wanda shi ne shugaban jam’iyyar Labour Party a Igumale cikin ƙaramar hukumar Ado ta jihar Benue.

Yadda ƴan bindiga suka kashe shugaban LP

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kashe marigayin ne yayin wani kwanton ɓauna da suka yi masa lokacin da yake dawowa daga gona tare da wasu mutum biyar.

“Su shida ne suka je gonar a kan babura guda biyu. Suna kan hanyar dawowa wajen ƙarfe 4:30 sai ƴan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna.”

“Ƴan bindigan sun tare su inda nan take suka harbe shugaban jam’iyyar wanda shi ne suka fara tunkara. Harbin da suka yi masa ya sa ya mutu a wurin. Sauran mutum biyar ɗin sun samu sun tsira ɗauke da raunika.”- Wata majiya

Me hukumomi suka ce kan harin?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, sakataren yaɗa labaran Labour Party na jihar Benue, Tersoo Orbunde, ya bayyana cewa an ɗauko gawarsa inda yanzu ake jiran a binne shi.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta bayyana cewa ba ta samu rahoto kan lamarin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here